Wakilan majalisar dokokin Nijar, sun kai wata ziyarar aiki jami’ar Damagaram, inda suka tattauna da daliban makarantar akan irin matsalolin dake ci masu tuwo a kwaya.
Sun kuma tabo batun tabarbarewar karabu a Damagaram, kamar yadda Sule Idi, mataimakin shugaban majalisar dokoki na hudu ya tabbatarwa muryar Amurka.
Bayan tattaunawa da dukkan wadanda abin ya shafa ‘yan majalisar sunyi alkawarin ganin cewa anyi sulhu.
A nasu bankaren daliban ta bakin shugaban kungiyar daliban jami’ar, Adam Ali Ali, yace tawagar wakilan sun nemi a yarjejeniya, yace sun amince amma idan za’a biya alwus alwus din dalibai kuma a ci gaba da biya ba wata matsala.
‘Yan majalisar sun yi kira ga Gwamnati da ta daidaita dukkan lamarin da ya shafi ilimi a jihar Damagaram
Su kuwa iyayen yara cewa suka yi sun fi kowa gamsuwa da ziyarar da ‘yan majalisar suka kai jami’ar domin ganin da ido, fatar su a kawo karshen matsalar dalibai su ci gaba da karatu cikin kwanciyar hakali