A shirinmu na nishadi, yau mun sami wani fitattacen jarumi ne da ya ga jiya ya ga yau a fagen wasannin kwaikwayo tun karnin da aka fara wassannin kwaikwayon Hausa.
Kasimu Yero, dai ya shafe kimanin sama da shekaru 40, da suka wuce kuma sun fara wannan wasa ne a matsayin sha’awa , tun lokacin da suke wasannin kwaikwayo a dandali, kafin shigowar akwatin talabijin.
Ya ce akwai bambanci tsakanin wasannin da ake yi a da, da na yanzu ta fannin harshe da ma yadda aka shirya labari, idan akayi la’akari da launin tufafi da ma gundarin labarin.
Kasimu Yero, ya ce marubuta a yanzu sun fi raja’a ne akan labarai da suka danganci soyayya, a cewarsa bayan malam Bahaushe yana da labarai da dama na al’adu da dabi’unsu idan aka dauke labaran soyayya.
Daga karshe ya kalubalanci masu harkar fim da suyi duba da ire-iren mutanen da labaran su keda amfani ga al’umma.