Taron masana na kara zurfafa bincike akan tsibirin tarihi na kasar Masar “Egypt” mafi akasarin mutane a wannan zamanin, basu da masaniyar yadda aka gina wadannan tsibirayen. Tsibirin Khufu “Pyramid” dake Giza, a kasar Egypt, ya kwashe tsawon shekaru fiye da ashirin ana gina shi.
Wanda aka samu damar kammala shi a shekarar 2560 B.C kamin bayyanar Annabi Isah. Yana da tsawon mita dari da arba’in 140 a tsayi, domin kuwa yafi sauran tsuburayen biyu girma. Shine tsibiri da mutun ya taba ginawa a fadin duniya da yafi girma.
Yanzu haka dai suna kokarin gano yadda aka gina wadannan tsuburayen, wanda yanzu haka suke kokarin shiga ciki, don ganin yadda tsakiyar su yake. Don kuwa an gina su da wadansu guma-guman duwatsu ne tun wancan zamanin.
Duk dai cikin binciken nasu, suna amfani da na’urorin zamani wajen ganin meke tsakiyar tsuburin. Ma’aikatar tarihi da binciken kayan al’adu ta kasar Masar, na bada hadin kai wajen zakulo abubuwan tarihi, da ya kamata mutane a fadin duniya su sani.
Wasu daga cikin abubuwan da suka gano zuwa yanzu, abubuwa ne da sun sabama tunanin mutun, anasa ran zasu bayyanar da sakamakon binciken su nan bada dadewa ba.