Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, dan jekan sakkwato, ya karrama wasu daga cikin nakasassu, 'yan jihar Imo, da suka samu nasarar lashe kyaututtukan Zinariya, a wasan “Rio Olympics 2016” da aka gabatar a kasar Brazil, watan da ya gabata.
Mr. Rochas, ya bama wadannan zakarun kyautar sababbin motoci da tsabar kudi, Roland Ezurike, Nwosu Ndidi da Orji Josephine, sun karbi makullan sabbabin motocin, su da tsabar kudi naira miliyan daya ga kowa cikin su.
Ya bayyanar da kokarin su, a matsayin wani abu da su kayi da ya jawo ma jihar su, suna da kasar baki daya. Don yana ganin cewar, idan har sauran matasa za suyi irin abun da wadannan sukayi, lallai da babu shakka kasar Najeriya, zata cigaba da rike sunan ta, a fadin duniya na kasar masu hazaka.
Haka kyautar tashi, bata tsaya kawai akan ‘yan wasan ba, har ta kaiga wadanda suke taimakama ‘yan wasan wajen horaswa. Kana yana kara kira ga matasa a baki daya kasar, da su maida hankali wajen nuna irin nasu baiwar da Allah, yayi musu a kowane bangare, don zama wani abu da kara darajar kasar su a idon duniya.