Kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru ashirin da uku ta Najeriya U-23 sun makale a jihar Atlanta nan kasar Amurka a hanayarsu ta zuwa wasannin motsa jiki na Olympic da za’a gudanar a kasar Brazil.
Wannan dai shine karo na biyu da kungiyar kwallon kafar ta Najeriya ta fuskanci irin wannan kalubale na rashin samun tikitin jirgi kamar yadda lamarin ya faru dasu ranar juma’a, inda suka gaza barin kasar ta Amurka.
Wata majiya ta bayyanawa shafin Africanfootball.com cewa daya daga cikin jami’an tawagar ‘yan wasan ya bayyana cewa suna iya bakin kokarin su domin tabbatar da kama hanya a yau talata.
Ya kara da cewa a lokacin da yake bada wannan rahoto, jami’a suna ma’aikatar wasanni ta Amurka domin tabbatar da samun tikitin tafiya.
Yaran kwach Samson Siasia dai zasu kara da kasar Japan ne a wasansu na farko ranar juma’a da misalign karfe 2:am biyu na safe lokacin Najeriya.