Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar JAMB Ta Janye Jerin Sunayen Data Mikawa Jami'o'in Kasar


Hukumar Jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB, ta janye sunayen daliban da ta mikawa jami’o’in kasar tun farko a matsayin wadanda za’a ba damar fara karatu a makarantun na wannan shekara.

A wani rahoto da hukumar ta fitar jiya lahadi, ta bayyana cewa ta dauki wannan matakinne domin tabbatar da cewa cibiyoyin manyan makarantun sun gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu na tantance sunayen daliban da suka can-canta kafin su mikawa hukumar, domin ta tabbatar da anyi aiki daidai da sharuddan shiga jami’o’in.

Sharuddan sun hada da la’akari da adadin yawan daliban da za’aba damar shiga manyan makarantun wadanda suka fito daga jihohin da ke fama da koma baya a harkokin ilimin zamani wadanda ake kira (Educationally disadvantage states) da kuma daliban da suka fito daga yankin da jami’o’in suke wato (Catchment areas) kamar yadda ministan ilimi Alhaji Adamu Adamu ya bada umurni a taron da kwamitin manufofin hukumar da aka gudanar kwanakin da suka gabata.

Bayanan da Dr Fabian Benjamin, ya rattabawa hannu kamar yadda mujallar Daily Post ta wallafa, sunce hukumar ta mikawa jami’o’in jerin sunayenne domin taimakawa wajan gudanar da ayyukan bada takardun shiga makarantunne akan lokaci, domin taimakawa sauran manyan makarantun gaba da sakandire gudanar da nasu ayyukan daukar daliban akan lokaci.

Bayanan sun kara da cewa kada dalibai su damu, wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren ayyukan daukar sababbin dalibai a wannan shekara ta 2016. Bayanan sun kara da cewa hukumar tace tayi nadama da duk irin damuwar da lamarin zai janyo wa cibiyoyin karatun gaba da sakandiren kasar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG