An lura da cewa yayinda shugabannin kasashen Afirka ke harramar tashi zuwa Kigali, babban birnin Rwanda, don fara taron kolinsu na wannan shekara, babban kalubalen dake gabansu shine zaben sabon shugaban Hukumar Raya Kasashen na Afrika.
Maccen dake rike da wannan mukamin a yanzu, Madam Nkosazana Dlamini Zuma ta Afirka ta Kudu, zata kamalla wa’adinta na shekarar hudu, ta sauka.
Izuwa yanzu akwai mutane ukku dake kwadayin darewa kan kujerar shugabancin Hukumar, wadanda biyu daga cikinsu ministocin harakUgandokin waje ne, daya daga Bostwana, na biyun kuma daga Equatorial Guinea. Na ukkun wani tsohon mataimakin shugaban kasar Uganda ne.
Ko bayan shugaban Hukumar. Taron zai bukaci ya zabi sabon mataimakin shugaban da kuma kwamishinoni har guda takwas.