Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Dabba Tasan Darajar Haihuwa!


Naman Daji Bear.
Naman Daji Bear.

Karen Williams, wata matashiya ‘yar-tsere tayi aron gama da wata kosasshiyar uwar naman daji “Bear“ a dai-dai lokacin da take gudu don neman zama ta daya a cikin jerin masu tsere, daga wani yanki zuwa wani yanki a cikin dajin “Valles Caldera National Preserve” a jahar New Mexico ta kasar Amurka.

A bayanin da ta gabatar a shafinta na facebook, Karen tace, tayi gudu na tsawon awowi inda ta kusa da karshen tseren don zamowa ta daya, sai taga wani jaririn bear ya makale, sai ta kokarta wajen bashi taimako.

Ana cikin hakan sai ga mahaifiyar jaririn tayo kan Karen, ta bugeta ta, Ita kuwa Karen, ta lura da cewar idan ta motsa ta nuna cewar alamun tana da rai, bayan irin dukan da bear din tayi mata, hakan zai iyasa ta kashe ta. Tayi kwanton bauna, na tsawon sa’o’I, masu yawa kamin masu agajin gaggawa su kawo kanta. An dai garzaya asibiti da ita don bata taimakon gaggawa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG