Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wata 'Yar Majalisar Dokokin Birtaniya


Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron
Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron

Halbe ‘Yar majilisar dokokin kasar Birtaniya mako daya kafin a gudanar da zazzafar muhawarar kuria'ar jin ra'ayin jama,a na ko kasar ta cigaba da kasancewa cikin kungiyar Tarayyar Turai ko a’a.

Wannan lamari ya sa kasar tayi sanyi a gwiwa, domin ko bata saba ganin harin bindiga ba ko kuma hargitsin siyasa mai muni ba.

Wasu wadanda suka ga halbin da a kayi wa wannan ‘Yar majilisar sunji makashin sai da yayi kuwa ya kira sunan Birtaniya kana ya harbe ta kuma ya kara da daba mata wuka wadda ya halban wato Jo Cox, karamar mamba ce a majilisar dokokin kasar.

‘Yar majilisar, yar shekaru 41, mai ‘ya’ya biyu, tsohuwar ma'aikaciyar aikin jin kai ce, kuma sananna a fannin yawan magana akan ‘yan gudun hijarar kasar Syria, kana bata boye ra'ayin ta game da ‘yan gudun hijira ba gaba daya, kuma tana sahun farko na sukan lamirin cewa Birtaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai.

Wannan baiwar ALLAH dai ta mutu duk ko da kokarin da aka yi na ceto ranta , a yankin gundumar ta, a jiya Alhamis.

Yanzu haka dai ‘yan sanda na binciken wannan al’amari, sai dai kuma jami'an gwamnati na kaffa-kaffa da danganta wannan kashin na jiya da abinda yake da nasaba da siyasa.

‘Yan sanda sukace sun kame wani mutun guda, sai dai basu samu wata kwakkwarar hujjar tuhumar sa ba tukunna, amma kuma suna nan suna neman karin wadanda ake tuhuma.

Sakatariyar cikin gida ta kasar ta Birtaniya tace ba zata ce uffan ba game da wannan kissan, har sai an samar da kwakkwaran madogara,

Tace kuma akwai bukatar dakatar da wannan muhawara ta cigaba da kasancewa cikin kungiyar Tarayyar Turai ko kasar ta fice har zuwa wani lokaci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG