Masana tattalin Arziki a Najeriya sunce taron Babban Bankin Najeriya tare da masana tattalin arziki shine na rage Darajar Naira mataki na wucin gadi abinda kuma zai haifar da tsadar Rayuwa a kasar.
Alhaji Shuaibu Idris, wani masani tattalin arziki yace taron da ya gabata a ganin sa abu daya mahimmi ana ta, ce ce ku ce kan maganar farashin Dala a kasar Najeriya.
Kai ya rarrabu farko akwai wadanda suke ganin cewa babu hujjar da za’a rage darajan Naira, kuma masu wanna ra’ayi suna gaini cewa kasashen duniya, da suka karya darajan kudaden su basu samu biyar bukata ba misali kasar Rasha, ta karya darajan kudinta da kimani kashi arba’in cikin dari amma har yanzu bata samu sauki bata kuma samu nasarar karya darajan kudi da tayi ba.
Kasar Misira a cikin watani hudu ta rage darjan kudin ta sau biyar amma duk da haka yana tangal tangal, saboda haka duk lokacin da wasu daga cikin masana tattalin arzikin suke ganin ya kamata a rage darajan kudi, wadanda suke ganin bai kamata ba sai suyi tayin tunanin cewa wace hujja mutun ke dashi na son karya darajan Naira.