Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barayin shanu sun rikide zuwa barayin mutane a jihar Kaduna


 Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.

Biyo bayan yadda gwamnatin Kaduna ta tarwatsa barayin shanu yanzu wadanda suka tsira sun rikide sun zama barayin mutane

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai yace gwamnatinsa ta tsarkake tsarin tsaro da ya samu kansa a wani mawuyacin hali a jihar can baya.

Gwamnan wanda yake amsa tambayoyin manema labarai, a wani taro na kaddamar da babura ga jami'an tsaro, yace ba wani abu ya kawo sace-sacen mutane ba a jihar illa yadda gwamnatin jihar ta tarwatsa barayin shanu.

Gwamnatin ta bada babura hamsin da daya da za'a raba tsakanin sojoji da 'yansanda da sauran jami'an tsaro. A ganin gwamnan harkar tsaro ta gyaru tun daga lokacin da ya karbi mulkin jihar. Yace lokacin da suka zo ana kashe-kashe a kudancin Kaduna da sace shanu amma yanzu sun yi maganinsu.

Abu sabo da ya taso a jihar yanzu shi ne maganar satar mutane da gwamnan ya ta'alakanta da canza salon barayin shanu da suka shiga satar mutane. Yace ita ma wannan matsalar jami'an tsaro suna nan suna aiki a kai kuma sai sun ga bayanta. Sabon kwamishanan 'yansandan jihar zai dora akan aikin da tsohon kwamishanan ya yi.

Shi ma kwamishanan rundunar 'yansandan jihar Adamu Ibrahim yace rundunar tana cigaba da samun nasara akan fatattakar barayin mutane a jihar. Ya godewa gwamnati bisa ga taimakon da take bayarwa domin inganta tsaro a jihar. Ya ce baburan da aka basu zasu yi anfani dasu kamar yadda ya kamata. Sun kama mutane da yawa da suke satar mutane.

Matsalar sace mutane ta fi kamari tsakanin Fulani inda ake sace masu mutane a ce sai sun biya kudi kafin a sakosu. Ana yi masu waya su biya miliyoyin nera kafin a sako mutanensu. Yawancin Fulani sun gujewa rugagensu sun koma cikin gari. Wata bafullatana da tace an kashe masu wata mata mai goyo tana roko a taimaka masu.

Mai ba gwamnan jihar shawara akan harkokin tsaro Kanar Yakubu Soja mai ritaya ya sanarda sabbin matakan da gwamnan ke dauka akan sace sacen mutane a jihar. Yace suna shirya kafa naurorin daukan hotuna a jihar. Zasu soma da garin Kaduna da Zaria da Kafanchan. Zasu kuma yi anfani da jiragen sama masu sarafa kansu da kansu dake dauke da naurorin leken asiri da tara bayanai.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG