Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dambarwar Siyasa Tsakanin PDP Da APC A Jihar Taraba


Sanata A'isha Jummai Alhassan.
Sanata A'isha Jummai Alhassan.

Yanzu haka dai ana cigaba da cecekuce a tsakanin gwamnatin PDP da kuma bangaren yan hamayya a jihar Taraba, inda gwamnan jihar Darius Dickson Isiyaku, ke kokarin hada kan al'ummar jihar ta hanyar kafa gwamnatin kowa da kowa, yayin da bangaren APC ke cewa an yi mata kwace.

Dinbin magoya bayan jam’iyyar PDP a wani gangami sun nuna farin cikin su game da nasarar da gwamnan jihar ya samu a Kotun Koli.

Sai dai kuma sabon gwamnan jihar Darius Dickson Isiyaku, yayi alkawarin cewa zai kafa gwamnatin adalci ba wai na jam’iyya ba, har ma ya bukaci wadanda suka sha kaye da suzo a hada hannu domin ciyar da jihar gaba.

A bangaren APC kuma Sanata Aisha Jummai Alhasan, wadda ta kalubalanci gwamnan jihar a Kotun Koli, tace ita fa kwace akayi mata. To amma ta bukaci bagoya bayan ta da su kwantar da hankulansu, su dauki kaddara.

Wannan danbarwa dai na zuwa ne yayin da ake haramar sake wasu zabuka na kujerun yan Majalisar Dokoki a jihar, wanda kuma lokaci ne kan iya tabbatar da jam’iyyar da zata kai labari.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG