Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Taron Yaki Da Miyagun Akidu Da Sunan Musulunci


Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau
Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Shugaban kungiyar Izala na Najeriya Shiek Abdullahi Bala Lau, yayi jawabi a sharar fagen taron yaki da miyagun akidu da sunan Musulunci, don samar da zaman lafiya musammam ma a kasashen da ke amfana da tafkin Chadi.

Za a gudanar da taron ne a tsakiyar watan gobe a Abuja, da hadin gwiwar Majalisar Musulunci da Duniya Rabita'atul alam islam, taron zai sami manyan malamai daga Saudiya da sauran sassan duniya.

Shiek Abdullahi Bala Lau, yace kokarin da gwamnatin Najeriya keyi ta yi dai dai, hakan ne yasa suka bi kasashen Afirka wanda suka hada kasar Benin da Nijar da Togo da Burkina Faso da Ghana don kira ga musulmai da su zo wannan taro don su bada kasidodi, su kuma nuna matsayin musulunci don gane da ta’addanci da sauran abinda akeyi da rigar musulunci.

Shima shugaban babban kwamitin shirya taron Dakta Bashir Isiyaku, yayi dirar mikiya kan tura yara su zama almajirai da sunan koyon karatun Alkur’ani, inda yace iyaye na da laifi don su suka haifi ‘ya ‘yan su da kuma tura su garuruwa masu nisa, batare da sanin inda ‘ya ‘yan su ke kwana ba ko abinda suke ci ko lafiyar su, hakan shike saka yaro ya tashi bashi da Imani da daukar munanan akidu.

Alkaluma daga cibiyar kididdiga ta Najeriya sun nuna akwai Almajirai dake gararanba kan tituna su miliyan 12 a Najeriya. kungiyoyin Ahlus sunnah sun dage wajen tsame akidarsu ta Salafanci daga cudanya da ta’addanci, don yadda ‘yan ta’adda ke fakewa da sunan Sunnah suna kashe mutane babu dalili.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG