Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Zama An Sace Lu'u-Lu'un Milliyoyin Kudi


Hong Kong Pink Diamond
Hong Kong Pink Diamond

An kama wata mata ‘yar kasar China, da ta saci lu’u-lu’u, wanda ya kai kimanin dallar Amurka $300,000. Dai dai da naira Milliyan sittin da shida 66,000,000. A babban birnin tarayyar Thai, Bangkok. An dai yi nasarar ciro lu’u-lu’un, da ta hadiye daga cikin hanjin ta.

Ta hadiye lu’u-lu’un ne, don ta samu damar fita da shi daga cikin kasar, ita dai matar ta sace lu’u-lu’un ne, a cikin wata kasuwar duniya inda ake baje koli, kana kuma ta maye gurbin lu’u-lu’un da wani na jabu. Wato ita dai matar an samu damar ganin ta ne a kyamarar bidiyo, dake zagaye da dakin. An kuma samu damar damke matar, da wani abokin tafiyar ta, a tashar jirgin saman Suvarnabhumi na garin Bangkok.

A tabakin jami’an ‘yan sanda, matar dai a karon farko, ta musanta abun da ake zargin ta da aikatawa, amma a lokacin da akayi hoton cikin ta, sai ga shi an ga lu’u-lu’un. Wannan yasa an bata magani don ta amayar da shi, hakan bai samu ba, sai da akayi mata wani karamin aiki aka ciro lu’u-lu’un. Wanda ya dauki kimanin minttoci goma sha biyu, yanzu haka tana asibiti tana samun sauki.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG