Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangin Matashin Da 'Yan-Sanda Suka Kashe Zasu Karbi Diyyar Dala Miliyan 6


Freddie Gray
Freddie Gray

Iyayen matashin nan bakin fata mai suna Freddie Gray, dan shekaru 25, da ya mutu kwanaki kadan, bayan dukan da jami’an ‘yan sanda sukayi mishi, wanda ya jawo zanga-zanga mai zafi a garin Baltimo a jihar Maryalan ta nan Amurka, a watan Afrilu da ta gaba ta. Zasu karbi kudin diyya da suka kai kimanin dallar Amurka milliyan shida da dugo hudu $6.4M kwatan kwacin naira Billiyan daya da milliyan dari hudu da takwas. 1,408,000,000.

A jiya dai Laraba, hukumomin karamar hukumar Baltimon, suka rattaba hannu a wannan yar-jejeniyar. Shugaban karamar hukumar Stephanie Rawlings, da kansiloli hudu ne suka sa hannu don a biya wannan kudaden. An bada wannan diyyar ne don a taimaka ma dangin wannan matashin da rashin dan su.

Shugaban karamar hukumar, ta kara da cewar wannan kudin da aka biya, basu da wata alaka da irin dukan da jami’an ‘yan sanda su shida sukayi ma wannan matashin, har da yayi sanadiyar mutuwar shi. Muhimmin dalilin biyan wadannan makudan kudaden, ba dan komai bane, illa don a kara kyautata zaman takewa a tsakanin al’ummar yankin da hukumomi.

Lauyan dangin mamacin, Mr. Billy Murphy, ya bayyanar da wannan a matsayin wani abu mai matukar mahimanci, da kuma nuna mutunta rayuwar dan’adam da karamar hukumar ta nuna. Duk dai da cewar bangaren jami’an ‘yan sanda na ganin wannan wani abu ne da bai dace ba, biyan dangin yaron makudan kudaden.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG