WASHINGTON, DC —
An roki matasan Najeriya da cewa a wannan karon, su yi hattara sosai, su kuma guji dukkan abubuwan da suka bata sunan matasa a zabubbukan da suka shige, watau tayar da fitina da satar kuri'u.
Wani matashin da ya tattauna da Dandalin VOA, Awwal Abdu Maje, yace babbar damuwar matasa a wannan karon, shi ne rashin tsaro a kasa, don haka suke da aniyar zaben shugabannin da suka san na kwarai ne masu kishin kasa da jama'a, wadanda kuma zasu yi kokarin tabbatar da tsaro.
Awwal Maje yace a bana, kudi ba zai yi tasiri a wannan siyasa ba, domin su kansu matasan sun farga da cewa amfani kawai ake yi da su a dada jefa su cikin mummunan hali na rashin abin yi, da sukurkucewar rayuwa.