Wani matashi mai sana’ar sayar da kayan chajin wayoyi me suna Khamisu Ibrahim, yayi kira ga matasa da su mai da hankali wajen yin sana’a don dogaro da kai, kada matasa su raina kowace irin sana’a.
Yace yafara wannan sana’ar tashine shekaru gomasha da suka gabata, wanda a cikin sana’ar har yake taimaka ma ‘yan’uwanshi da danginshi, hasalima a cikin wannan sana’ar ne yasamu har yaje yayi karatunshi har zuwa matakin sakandire a yanzu.
Kuma babban burinshi shine ya zama wanda zai taimakama al’umah baki daya. Ya kara da cewar matasa yakamata su riki gaskiya a kowane hali suka samu kansu, wanda ta rikon gaskia ne kawai za’a iya samun cigaban kasa da al’umah, don ya tabbatar idan badan riko da gaskiya da yayi ba, to lallai da bai kai yadda yake ba yanzu. A karshe yayi kira da gwamnatoci da masu hannu da shuni da su dinga taimaka ma matasa don dogaro da kai.