Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Kada Ku Rena Sana'a Komin Kankantar ta


Wata baiwar Allah me suna Hajiya Hauwa Mohammad, ta kwashe sama da shekaru goma sha biyar tana sana’ar saida yaji, ita dai Hajiya Hauwa, tace wannan sana’ar da take yi tayi mata komai don da wannan sana’ar ta yi abubuwa da dama, wanda a yanzu haka diyar ta tana zuwa makaranta wanda kuma duk da ga cikin arzikin yaji ne take wannan hidindimun.

Ta ce bata da bukatar daukan bashin banki don habaka sana’ar ta, tace dai dan jalin da take da shi ya isheta gudanar da sana’ar. A cikin wannan sana'ar ta koyar da mutane da dama yadda zasu inganta wanna sana'ar, ta kuma koyar da su ta yadda zasu inganta wannan sana'ar su dinga sa wannan yajin a cikin mazubi me inagnci. Tace babban burinta shine ta kara koyar da mutane da dama don suma su iya dogaro da kansu.

Tayi kira da mata da su kama sana’a koda kuwa da jali dan kadaune, domin tayin haka ne kawai zasu iya gujema talauci a cikin rayuwa. Kuma wannan wata hanya ce da zasu taimakama tattalin arzikin kasar baki daya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG