Dubban sojojin Chadi sun tsallaka cikin Kamaru domin taimakawa kasar wajen yakar ‘yan ta’addar Boko Haram na Najeriya.
Sa’id Abdoulkarim dake aiki ma gidan rediyon gwamnatin Kamaru a garin Kousseri dake bakin iyaka da Chadi, ya fadawa VOA cewa yau asabar da safoiya ne dubban sojojin Chadi suka shiga cikin Kamaru a wata kwambar motocin soja.
Yace sojojin sun a kan hanyarsu ta zuwa garin Maroua, daga inda zasu rika yin aiki tare da sojojin Kamaru. Yace an gudanar da wani gagarumin gangami a Chadi domin nuna goyon baya ga kasar Kamaru a yakin da take yi da Boko Haram.
Kakakin rundunar sojojin Kamaru, Kanar Didier Badjeck, yace daga garin Maroua za a rika girka sojojin na Chadi a bakin dagar yaki da Boko Haram a kan iyaka da Najeriya. Yace zasu yi aiki tare da sojojin Kamaru wajen murkushe duk wani yunkurin Boko Haram na kutsawa cikin Kamaru.
A ranar laraba ne Chadi ta ce zata tallafawa Kamaru, wadda shugabanta Paul Biya yayi rokon da a hada kai a tsakanin kasashe domin yakar Boko Haram.