Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Mota Da Bama-Bamai Masu Yawa Yau A Gombe


Motar A Kori Kura Da Aka Kama Da Bama-Bamai 5 Ciki A Gombe, Jumma'a 16 Janairu 2015
Motar A Kori Kura Da Aka Kama Da Bama-Bamai 5 Ciki A Gombe, Jumma'a 16 Janairu 2015

'Yan sanda a Jihar Gombe, sun kama wata motar a kori-kura dauke da bama-bamai har guda 5 a cikinta.

An kama wannan mota mai dauke da lambar Jihar Lagos da safiyar yau a kan hanyar zuwa garin Dadinkowa a babban birnin na Jihar Gombe, inda aka boye wadannan bama-bamai a karkashin buhunan masara, da katifu da sauran tarkacen kaya na gida a kokarin batar da sawu domin kada a gane.

'Yan sanda sun yi maza suka warware bama-baman, suka kuma kama direban motar.

Kakakin 'yan sandan jihar Gombe, DSP Fwaji Attajiri, yace da asubahin sun yi saurin kange wannan wuri yayin da kwararru suka nazarci bama-baman kafin su warware su.

Yace wadannan bama-baman an dana su cikin wasu sundukan da zasu kai tsayin mutum ko zuwa kirjinsa.

Yayi kira ga duk jama'ar jihar Gombe da su ci gaba da sanya idanu kan irin wadannan 'yan ta'adda, domin aikin na kowa da kowa ne ba 'yan sanda kawai ba.

'Yan Sandan Gombe Sun Kama Mota Dauke Da Bama-Bamai - 2'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG