Ana ci gaba da kwashe gawarwakin wadanda suka mutu tare da mkutanen da suka ji rauni a sanadin tashin wani bam cikin daren nan na Jumma'a a dab da kasuwar mata dake unguwar Arawa a garin Gombe.
Bam ya tashi dab da lookacin sallar Isha, amma ya zuwa yanzu babu cikakken bayani a kan ko an dasa bam din ne aka bar shi a wurin, ko harin kunar bakin wake ne, ko kuma dai ya tashi ne bisa kuskure.
Mun tattauna da wani dan unguwar Herwa Gana a Gombe, Garba Tela, wanda dan siyasa ne, da kuma wakilinmu na yankin, Abdulwahab Muhammad, wadanda suka yi mana cikakken bayani a www.dandalinvoa.com na abubuwan da suka faru kuma suke faruwa.
Idan ba a manta ba, a yau din da asuba ne 'yan sanda a Gombe suka kama wata mota dauke da bama-bamai har guda 5 a cikinta. Shin ko akwai alaka a tsakanin wadannan abubuwa biyu?
A saurari bayani.....