Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hawainiyar Dokubo Asari Ta Kiyayi Ramar 'Yan Arewa


Mujahid Dokubo Asari
Mujahid Dokubo Asari

Wata kungiyar kare muradun 'yan arewacin Najeriya ta ja kunnen tsohon madugun tsageran yankin Niger-Delta, Mujahid Dokubo Asari, da yayi taka tsantsan a irin babatu da bakaken maganganun da yake furtawa kan 'yan arewa.

Kungiyar da ake kira ACAC a takaice, ta ce duk wani abinda Dokubo Asari yake takama da shi, to 'yan arewa su na da fiye da shi, kuma ba shi kadai ne ya san yadda ake tashin hankali ko zaman lafiya ba.

Shugaban kungiyar, Comrade Aminu Adam, yace babu wanda yake tsoron a raba Najeriya, amma Dokubo Asari ya kwana da sanin cewa ko dai ya daina batunci da bakaken maganganun da yake fadawa 'yan arewa, ko kuma zasu mayar da martanin da ya fi nasa zafi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG