Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Matsala ga Batun Katin Zabe a Jihar Neja


Kimanin mako guda kennan da hukumar zaben Najeriya, ta fara raba katin jefa kuri’a, na dindindin a jihar Neja, amma har yanzu jama’a da dama basu karbi nasu katin ba.

Hatta Gwamnan jihar Mua’zu Babangida Aliyu, ya koka game da yadda ake gudanar da aikin bada katin zaben. A lokacin da yaje majalisar dokokin jihar Neja, domin mika kasafin kudin shekarar 2015.

Gwamnan yace a cikin kanana hukumomi guda ashirin da biyar guda goma sha daya ne kawai aka kawo, kuma babu inda aka samu daidai.

Itama dai majalisar dokokin ta Neja, ta na shirin daukar mataki akan wannan lamarin.

Tuni dama jami’yyar, adawa ta APC, tace ama dakatar da bada katin ganin bata gamsu da yanda lamarin ke tafiya ba.

Jami’in watsa labarai na hukumar zabe a jihar Neja, Madaki Muhammad Wase, yace hukumar ta gamu da wasu matsaloli ne amma yanzu an shawo kansu.

Katin Zabe - 3'334"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

XS
SM
MD
LG