Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Arewa Sun ja Kunnen Asari Dokubo


Wasu matasa
Wasu matasa

A Yayin da ake shiga sabuwar shekara 2015, da za’a yi zabubbuka a Najeriya, wasu kungoyoyin matasa sun fara kira ga ‘yan siyasa sunyi kokarin ganin sun iya bakinsu, domin gujewa tada hankalin da zai iya jawo sanadin salwantar rayuka da dama.

Malam Aminu Sule, daya daga cikin ‘ya’yan wata kungiyar mai suna “Network for Justice” a turance, mai hankoron ganin an samarda shugabanci mai adalci a Najeriya, ne ya furta haka ga wakilin muryar Amurka.

Ya kuma ce ya zama wajibi, ayi kokarin gaini cewa ba’a maimaita irin rikicin da aka samu a zabubbukan 2012, ba.

Sai dai kuma duk da irin gargadin da ake yi, game da kalmai dake fitowa daga bangarori daban-daban na Najeriya, game da zaben 2015, wata kungiyar matasan arewacin Najeriya, mai suna ACAC, ta gargadi Asari Dokubo, a wata hira da Babban jami’in kungiyar Komrade, Aminu Adams, yayi da wakilin muryar Amurka, Isah Lawal Ikara, ya ce Asari Dokubo, ya kiyayi Arewacin Najeriya, da furucinsa, cewa suma suna daidai dashi.

Matasan Arewa - 3'13"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

XS
SM
MD
LG