Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Labaran Najeriya A Wannan Safiya Ta Laraba


Maharba da Kayan Yakinsu, 14 ga Nuwamba 2014.
Maharba da Kayan Yakinsu, 14 ga Nuwamba 2014.
  • Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Gombe, Abdullahi Kudu, yace lallai an ci sa’a da aka tare mutumin da yayi niyyar kai harin bam cikin tashar motar Gombe Line dake garin Gombe kafin tashin bam din da ya boye cikin wata jaka…Yace, "a cikin jakar tasa, mun ga kundojin gurneti guda 5, da kwanson bam guda biyu, da cylinder biyu da kuma kunamun tayar da bam guda biyar. Mun godewa Allah cewa mun samu nasarar warware wannan hade-haden." Matasa a tashar motar dai sun samu nasarar kama wanda yayi niyyar tayar da wannan bam din, suka kuma lakkada masa duka kafin su kona shi kurmus.
  • A makwabciyar Gombe, Jihar Adamawa, maharba da ‘yan bangar da suka fara yunkurin kawar da Boko Haram, cikinsu har da wata mace maharbiya, sun roki jama’a da su kara bayar da hadin kai wajen zakulo ‘yan bindigar da suka hana jama’a sakat a wannan yanki. A wani gefen, jama’a da dama sun ce kyale jama’a su kare kawunansu abu ne mai kyau, kuma ya kamata a gaggauta tallafawa wadanda suka kuduri aniyar kare jama’a kamar maharba da ‘yan Civilian JTF
  • Daga Abuja, majalisar dattijan Najeriya zata sake yin zama yau laraba domin tattauna rokon shugaba Goodluck Jonathan na kara wa’adin aiki da dokar ta baci, a bayan da ta kasa cimma matsaya kan wannan batu jiya talata. Sanata Sahabi Ya’u daga Jihar Zamfara yayi Karin bayani da cewa dokar ta baci ba ta tsinana abinda ake so ba, amma in an cire ta, da me za a maye gurbinta? Wani tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Borno, Dr. Haruna Yerima, yace kamata yayi a sake lale game da batun dokar ta bacin.
    Labaran Najeriya A Safiyar Yau Laraba - 3'30"
    please wait

    No media source currently available

    0:00 0:03:30 0:00
    Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG