A yau laraba ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya zasu karbi bakuncin Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu, a wasan karshe na rukunin share fagen shiga gasar cin kofin kasashen Afirka da za a yi a kasar Equatorial Guinea nan da watanni 2.
Wannan wasa da za a gwabza shi yau da karfe 6 na maraice a filin wasa na garin Uyo a Jihar Akwa Ibom, yana da matukar muhimmanci ga ‘yan Super Eagles na Najeriya wadanda sune na biyu a rukunin A, a bayan ‘yan Afirka ta Kudu masu maki 11. Duk yadda wasan na yau zai kasance dai, Afirka ta Kudu ta riga ta tsere ma sauran kasashen dake wannan rukuni, Najeriya da Kwango masu maki 7-7 da kuma Sudan mai maki 3.
Idan har ‘yan Super Eagles na Najeriya ba su samu sun lashe wasan yau din ba, to akwai yiwuwar cewa watakila ba zasu iya tafiya Equatorial Guinea ba idan har Kwango ta samu ta doke Sudan a wasan da su ma zasu buga a yau din kasancewar ita ma maki 7 gare ta kamar ‘yan Super Eagles.
Wannan ne ma ya sa har kwach din ‘yan Flying Eagles na Najeriya, Samson Siasia, ya ja kunnen ‘yan wasan na Super Eagles da kada su yi sake su bar ‘yan Bafana Bafana su fara jefa musu kwallo a raga, ko kuma su yi ta rike kwallon.
Ya zuwa yanzu dai a bayan Afirka ta Kudu, sauran kasashen da aka tabbatar zasu shige zuwa gasar sune mai masaukin baki Equatorial Guinea, da Cape Verde wadda ta lashe rukunin F da Zambia mai bi mata baya, sai Aljeriya da ta lashe rukunin B, sai Tunisiya da Senegal dake saman rukunin G, da Burkina Faso da gabon dake saman rukunin C, sai Cameroon da ta lashe rukunin D.