Dalilin taron shi ne ta fadakar da jami'an kiwon lafiya daga jihohi a matakin karkara ta yadda zasu wayar da kawunan jama'a akan cutar ta ebola.
Dangana Sa'adu babban jami'in dake kula da jihohin arewa maso tsakiya a hukumar kiwon lafiya na matakin farko ya bayyana dalilin kiran taron. Yace an kira taron ne domin jihohi su gane cewa cutar ebola tana nan kana a koya masu yadda zasu sanar da kowa a birane da kauyuka yadda za'a yi tsafta domin a gujewa cutar.
A wani hali kuma gwamnatin jihar Neja ta sanya kwamitin fadakarwa game da cutar tare da shirin ganawa da limaman Musulunci a jihar domin daukar mataki kafin a yiwa gawa jana'iza.
Kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Hajiya Hadiza Abdullahi tace yanzu suna son su yi magana da limamai da jama'a domin a muslunce ranar da mutum ya rasu ranar za'a yi masa wanka a binneshi to amma illar gawan wanda ya rasu sanadiyar cutar ebola ta fi muni. Tace wanda ya taba gawar da wanda ruwan gawar ya taba duk zasu kamu da cutar. Sabili da haka suke so a gwada gawa kafin a binneta.
Kula da iyakoki da jihohi da jamhuriyar Benin na cikin matakan da jihar Neja ta dauka. Kwamishanan yada labarai Alhaji Inda Yabo yayi bayanin damuwarsu inda yace cutar kanjamau da aka ce ita ce tafi muni idan mutum na shan magani sai yayi shekara da shekaru a raye. Amma cutar ebola farar daya take kashe mutum. Jihar zata bayyana cibiyoyin da aka kebe domin tantance marasa lafiya domin sanin irin cutar da suke fama da ita.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.