Shugaban kungiyar na kasa, Misbahu Lawan Didi, yace duk yaron da ya kaucewa karbar maganin a duk zagaye guda na yin rigakafin, yana jefa kansa da sauran yara cikin kasadar kamuwa da kwayar cutar dake haddasa wannan nakkasa.
A lokacin da yake magana a madadin wannan kungiya ta su mai dubban membobi a fadin Najeriya, Malam Misbahu yace a yanzu haka Najeriya ce kadai kasar Afirka da ta rage inda wannan cuta ta Polio ta yi katutu. Yace idan har ba a samu an murkushe wannan cuta a Najeriya ba, to sauran kasashe makwabta ma su na iya harbuwa da ita.
Kungiyar ta kaddamar da wani gagarumin gangami nata na tabbatar da cewa an samu nasarar ayyukan rigakafin wannan cuta a jihohi 15 da suka fi fama da Polio a arewacin Najeriya.