Babban darektan Hukumar Kiwon Lafiya Matakin farko ta Najeriya, Dr. Ado Gana Muhammad, ya fadawa taron cewa rabon da a samu wani dauke da jinsin kwayar cutar Polio da ake kira Type3 tun watan nuwambar shekarar da ta shige. Haka kuma yace yawan jinsunan kwayar cutar da ake gani sun ragu daga 14 sun komo 2 kawai.
Dr. Muhammad ya bukaci majalisar da ta fito da sabbin hanyoyi da fasahar rigakafin da kowa zai iya aiwatar da shi ba sai kwararru ba kawai domin a samu kaiwa ga karin yara.
Yace najeriya tana son gaggauta yin amfani da sabbin magungunan rigakafi, sai dai ya lura da cewa sabbin allurai na rigakafi, bisa al’ada, sun fi tsada.
Sai dai kuma Dr. Muhammad yace har yanzu akwai kalubale a gaban kasar nan, musamman a fannin tsaro, a wasu kananan hukumomi 10 a Jihar borno da kuma a Jihar Yobe, inda aka kafa dokar-ta-baci. Yace gwamnati ta kirkiro da sabbin dabarun yaki da cutar a arewa, musamman a yankin arewa maso gabas.