Jami'an sun yi rokon da a bayar da cikakken kudin aiwatar da wannan shirin domin tabbatar da cewa an ga bayan wannan cuta.
Ministocin, wadanda suka halarci Taron Kiwon lafiya na Duniya na 66 a Geneva dake kasar Switzerland, sun nuna gamsuwa da ci gaban da aka samu a shekarar da ta shige wajen rage wannan cuta zuwa matsayin da bai taba saukowa ba, a saboda irin matakan da kasashe ke dauka.
A makon da ya gabata ga misali, ba a samu rahoto ko kwaya daya na kamuwa da cutar Polio a duk fadin Najeriya ba.
Kasidar baya-bayan nan ta mako-mako da ake bugawa kan yaki da cutar Polio, Weekly Polio Update, ta ce a cikin makon da ya gabata, ba a samu sabon rahoto na kamuwa da kwayar cutar polio jinsin WPV ba.
Ta ce yawan wadanda suka kamu da wannan kwayar cutar a 2013 yana kan 22 ya zuwa wannan lokacin. Mutane na baya-bayan nan da aka samu da kwayar cutar Polio ta WPV sun bulla ne a jihohin Borno da Taraba a karshen watan Afrilu.