Mr. Obama zai gana da takwaransa na kasar Burma Thein Sein da kuma Aung San Suu Kyi, babbar ‘yar gwaggwarmayar rajin damokaradiya ta kasar, wadda aka saki a shekara ta dubu biyu da goma bayan ta shafe shekaru 15 karkashin daurin talala.
Shugaba Obama yace ziyarar da zai kai kasar Burma ba yana nufin yana goyon bayan gwamnatin bane, sai dai nuna na’am da garambawul da ake yi a tsarin siyasar kasar.
Mr. Obama yace an nuna niyar yin garambawul a harkokin siyasar kasar Burma saboda haka ya kamata a karfafa masu guiwa.
Yace gurin ziyar tasa ita ce ya nuna irin cin gaban da aka samu, da kuma tattaunawa a kan matakan da ya kamata Burma ta dauka nan gaba.