Ana ci gaba da zaman dar-dar a garuruwan Damaturu da Kaduna Nigeria.
Mazauana manyan biranen Arewacin Nigeria biyu, Kaduna da damaturu na ci gaba da zaman dar-dar yau laraba, bayan kwanki ukun da aka yi ana tafka hargitsin da ya janyo mutuwar mutane masu yawa.
An kuma maido da dokar hana yawo a Kaduna da Damaturu har tsahon sa’o’i 24, abinda ya maida titunan biranen biyu Fankan-Fayau. Im banda tulin soja ba wanda ake gani a kan tituna.
Ana samun rahotannin dake sabawa juna cewar adadain yawan wadanda suka rasa rayukansu yayi sama daga 80 zuwa 95.Tun ranar lahadin da ta gabata ce ake tafka hargitsi bayan da kungiyar Boko Haram ta bada sanarwar daukan alhakin kai hare-haren da suka lalata mujami’un Kirisya guda uku dake Kaduna. Inda kuma aka sami wani dan kunar bakin wake ya kai harin da ya janyo asarar rayukan mutane 21 domin maida martini.
Rikicin ya watsu zuwa Damaturun jihar Yobe a ran litinin.
Hukumomin Nigeria sun aza bazuwar hargitsin a kan sassan biyu Musulmi da Kirista maras sa hakurin zama da juna.
A saurari rahoton wani rahoto daga Damaturu, kan hali da mutane suke ciki, biyo bayan kafa dokar hana fita.