Jami’ai a yankin arewacin Najeriya sun ce a yanzu mutane kimanin hamsin aka kashe ranar lahadi a hare-haren da aka kai kan wasu majami’u guda uku, da kuma daukar fansar da ta biyo baya a Jihar Kaduna.
An kashe mutane akalla 21 a hare-haren bam na kunar bakin wake da aka kai a Zaria da Kaduna. Daga bisani, matasa mabiya addinin Kirista sun bazu a titunan Kaduna, su na cinna wuta a masallatai da kantuna, da kuma kai farmaki a kan motoci, inda aka kashe mutane akalla 29.
Wannan sabon adadi na mutanen da aka kashe jami’an ayyukan gaggawa ne suka bayar da shi jiya litinin bisa sharadin cewa ba za a bayyana sunayensu ba.
Wani sakon Email da aka samu daga hannun wani mai suna Abul Qaqa, mai ikirarin cewa yana magana ne da sunan kungiyar na ta Boko yace kungiyar ce ta kai hare-hare kan majami’un domin fansar lalata masallatai da kuma kashe Musulmin da ta yi zargin kiristoci sun yi.
Jiya litinin da maraice, mazauna garin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, sun bada rahoton jin kararrakin fashe-fashe da harbe-harbe. Ba a san ko an hallaka mutane a wannan lamarin ba, ko kuma yana da wata alaka da tashin hankali a Kaduna.