Yana yiwuwa Majalisar Dinkin Duniya zata fara tattaunawa kan batun ranar Laraba yayin taron kolin Majalisar a birnin New York kan halin tsaro a yankin Sahel na nahiyar Afirka.
Da yake magana a wani dandali na dabam wajen taron kolin Majalisar Dinkin Duniya jiya Litinin, firai ministan harkokin kasashen ketare na kasar Faransa, Laurent Fabius yace kasar Mali ta nemi a tura mata dakarun ne a wata wasika da ta rubutawa babban magatakardan Majalisar ranar goma sha takwas ga watan Satumba.
Farkon wannan makon, gwamnatin kasar Mali da kuma kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS suka amince da tura dakarun yammacin Afrika a karkashin wani shiri na Majalisar Dinkin Duniya. Wannan ya bada damar samun amincewar Majalisar Dinkin Duniya.