Wata mata ‘yar darikar katholika wace ta sadaukar da rai domin coci, ‘yar kasar Columbia daka sace a akudancin Mali kusan shekara daya yanzu, ta fito cikin fefen vidiyon masu ikirarin jihadi, tana kiran da Papa Roma ya saka baki a sako ta.
Mutane 36 suka mutu wasu 200 kuma suka jikkata a wata arangama tsakanin ‘yan aware da dakarun gwamnati.
Shugabannin kungiyar hadin kan kasashen Afirka sun kaddamar da yarjejeniya akan sufurin jiragen sama da nufin samar da rahusa a tafiye-tafiyen jiragen sama a Nahiyar Afirka
Labaran Duniya a takaice
Majalisar Dinkin Duniya da shugabannin Afirka, sun hadu a taron kolin kungiyar, domin tattaunawa kan hadin kai da kuma tabbatar da shirin wanzar da zaman lafiya da dakarun Majalisar Dinkin Duniya ke yi wajen yaki da masu tsatsauran ra’ayi.
Sai kuma a Burkina Faso inda Gidauniyar Melinda Gates ta ba da sanarwa tallafin dala miliyan $45 domin shirye shiryen tsarin Iyali da samar da abinci mai gina jiki a Burkina Faso.
A kasar China masu ayyukan gine gine su 1500 ne suka kammala gina tashar jiragen kasa a cikin sa'o'i 9.
An gudanar da bikin rantsar da sabon shugaban kasar Liberia, George Weah, ranar 22 ga watan Janairu, 2018
George Weah ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayinsa na sabon shugaban kasar Liberia a zabe na farko da aka sami sauyin gwamnatin dimukradiyya cikin lumana tun bayan shekarar 1944.
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya ce za su maida ofishin Jakadancin Amurka Zuwa Qudus a karshen badi, lamarin da ya haifar da bore daga Larabawa ‘yan majalisar Isra’ila.
Shirin da ke zuwa duk mako domin fadarwa da nishadantarwa.
A Amurka hukumar kulla da manyan laifufka ta Amurka wato FBI tace shugabanin yan bangan MS-13 na yankin tsakiyar Amurka wadda keda magoya baya kusan dubu 10 a nan Amurka na ci gaba da nuna bakin ciki bayan da ake ci gaba da kama wasu cikin shugabanita dake nan Amurka.
Domin Kari