A Najeriya wasu mata uku na kungiyar Super Eagles na shirin halarta taron wasanin hunturu na Olympics a karon farko a cikin tarihin kasar.
'Yan wasan Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu mata zasu shiga gasar wasar Olympic ta hunturu da za’a yi a Pyeonchang a karkashin tuta daya
A Najeriya daruruwan mutane suka yi zanga zanga a Abuja babban birnin kasar suna kira a saki shugaban ‘yan Shi'a Shaikh Ibrahim EL Zakzaky da yake tsare tun shekarar 2015.
Shugaba Ali Bongo Ondimba ya gana da firayin ministan kasar ChinaWang Yi, a Libreville, inda y ace yana fatan China zata ci gaba da taimakawa domin samar da ci gaba a kasar sa.
LIBYA: akalla mutane 20 suka hallaka wasu sama da 60 kuma suka ji raunika a wata arangama tsakanin ‘yan bindiga da jami’an tsaron gwamnati a filin saukar jiragen saman kasar Libya na kasa da kasa dake birnin Tripoli.
Boko Haram ta saki sabon bidiyo da ke nuna akalla ‘yan matan makarantar Chibok 14 inda daya daga cikinsu ta ce shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya aurar da su
Akalla mutane 21 suka mutu kana wasu 38 suka jikkata bayan da wata motar bas ta kauce a hanya ta bigi wata bishiya a yammcin Kamaru.
A Jamhuriyar Demokratiya Congo hukumomi na ci gaba da kokarin shawo kan barkewar cutar kwalera da ta mamaye wasu kauyuka da dama dake fama da tashe tachen hankula a yankin Kinshasa babban birnin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar muntane 28 wasu 411 sun kamu da cutar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya cewa yan majalisu a wani zaman tattaunawa kan maganar baki yan gudun hijira cewarsa ya komace baki daga kasa kamar Norway, ba daga lalatatun masakai kasashen Afirka ko kuma Haiti da Elsalvador, duniya gaba daya ta yi Allah waddai da wanan magana.
daliban Jamhuriyar Nijar suna nan suna zaman dirshan don bijirewa rashin iya shugabancin shugaban Jami'ar Zinder.
A yammacin kogin Jordan daruruwan yahudawa ne suka halarci janaizar Raziel Sheva, limamin yahudawa dan shekaru 35, da aka kashe a daren Talata, da ta gabata a kusa da sansanin ‘yan share wuri zauna da ake kira kira Havat Gilad dake kusa da Karin Nablus.
Kwamitin majalisar dokokin Afirta ta kudu ta wani kwamitin majalisar dokokin kasar tana muhawara kan daftarin kudurin tsige shugaban kasa dake kan gado; zargin cin hanci da rashawa ya dushe martabar shugaba Jacob Zuma.
NIGERIA: ‘Yan sandan Najeriya sun harba hayaki mai sa hawaye da kuma yin arangama da Musulmi ‘yan shi’a da suke zanga zanga a ranar litini a birnin Abuja.
Domin Kari