Gwamnatin hadaka mai mulki a Habasha ta zabi Abiy Ahmed ya zama shugabanta, wanda hakan ya ‘dora shi a hanyar zama fara minista nan gaba. Ahmed shine ‘dan kabilar Oromo na farko da ya taba zama shugaba cikin shekaru 27.
Australia: Jakadan Rasha, Grigory Logvinov yace duniya zata shiga yanayin zaman doya da manja inda har kasashen yamma suka ci gaba da mayar da Rasha saniyar ware.
‘Yan sandan Kenya sun tsare dan jam’iyar adawa Miguna Miguna a filin tashen jirage, ana zargin shi ne da laifin cin amanar kasa, inda aka fitar da shi daga kasar watan Fabrairu saboda goyon bayan da ya nuna wa shugaban ‘yan adawa Raila Odinga.
Rahotanni sun ce wata babbar tawagar jami’an gwamnatin Korea ta Arewa ta kai ziyarar Beijing, inda wasu kafafen yada labarai ke cewa shugaba Kim Jong Un ne, yayin da wasu ke cewa kanwarsa c eke jagorantar tawagar.
Duniya: Manyan shugabannin kasashen Duniya da suka hada da na Amurka da Turai sun kori jami’an diplomasiyyar kasar Rasha da dama sanadiyar sakawa wani tsohon jami’in leken asiri guba a Birtaniya.
EGYPT: A yau Litini aka bude rumfunan zabe domin kada kuri’u a zaben shugaban kasa da za a kwashe kwanaki uku ana yi, zaben da ake tunanin shugaba el Sisi zai yi nasara akan abokin hamayyarsa Mousa Mustafa Mousa
Gwamnati ta ce Boko Haram ta maido da dalibai 101 daga 110 da suka sace a garin Dapchi a watan da ya gabata.
Afghanistan: Akalla mutane 26 suka mutu wasu 20 kuma suka jikkata bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa nakiyarsa a gaban jami’ar Kabul.
Shugaban China Xi Jingping ya yi jawabin kishin kasa mai jan hankali, a taron majalisar wakilai ta kasar wanda aka yi a karo na 13, inda ya yi kira ga China da ta tashi tsaye wajen kimar da ta cancance ta a idon Duniya.
Ana zargin dakarun Najeriya da yin watsi da gargadin da aka musu na cewa akwai yiwuwar mayaka Boko Haram za su kai hari a Dapchi, inda aka sace dalibai mata 110.
Shugaba Vladimir Putin sake yin nasara da gagarumin rinjaye a zaben shugaban kasar Rasha, wanda ya kara wa’adin mulkinsa na shekari 6
A Madagascar A kalla mutane 17 suka mutu, sama da 6,000 suka rasa muhallansu a sakamakon mahaukaciyar guguwar “Eliakim” da ta ratsa tsibirin a cikin karshen mako.
Domin Kari