France: Masu zanga zanga sun taru a birnin Paris bayan da wani Shugaban kungiya Laurent Berger ya zargi Shugaban Faransa Emmanuel Macron da yin watsi da kungiyar a sausauyen da ya ke yi a kasar.
Chad: 'Yan Majalisar Dokoki sun amince da wani kudurin doka, mai kara ma Shugaba Idriss Deby iko da kuma damar cigaba da mulki har zuwa 2033.
RWANDA: Tsohuwar shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf, ta sami kyautar Ibrahim MO ta shekarar 2017, a bin da aka gudanar a Kigali.
AFGHANISTAN: Fashewar wasu tagwayen bama-bamai a Kabul sun hallaka akalla mutane 26, wanda suka hada da wasu ‘yan jarida 9, kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.
Nigeria: Kimanin mutane hudu ne suka mutu a wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a Birnin Maiduguri dake Arewa maso Gabashi.
Korean Peninsula: A Koriya shugabannin kwaminisanci dake Arewa dana dimokaradiyya dake Kudu , suna zaman tattaunawa mai dinbin tarihi inda suka bada sanarwar yarjejeniyar tabbatar da ruguza yunkurin Nukilya da wanzaar da zaman lafiya
Rangadin da tawagar shugaban ma'aikatar gandun daji keyi a duk fadin kasar Nijar, domin fadakar da al'umma a kan shuka itace da kuma tattalinsu.
Amurka: Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya gargadi Shugaban Amurka da yaci gaba da aiki da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 ko kuma zai “dandana kudar shi” a yayin da lokacin sabunta yarjejeniyar ke gabatowa..
Afirka ta Kudu: Jami’ai sun bada sanarwar cewa tsohon shugaban Amurka Barak Obama ne zai gabatarda jawabin taron shekara-shekara na bana na tuna marigayi Nelson Mandela a watan yuli a Johannesburg.
Domin Kari