Ana kokarin wayarwa matasa kai da su guji bangar siyasa, su yi amfani da karfin kuri'unsu domin kawo sauyin da suke nema.
Nigeria: ‘Yan sanda sun harba borkonon tsohuwa kan ‘yan shi’a da ke zanga-zangar neman a sako shugabansu.
Yemen: Gwamnatin Saudiyya ta yi wa ‘yan Tawayen Houthi gargadin za ta mayar da martani idan suka ci gaba kai mata hare-haren sama.
A kalla dakarun Afurka, da na Amurka da tarayyar Turai 1500 su ka yi atiseye domin yakar barazanar ta'addanci a yankin.
Ya Makomarsa Za Ta Kasance Gobe? Muryar Amurka ta tattauna kan wannan batu yayin zagayowar shekaru 75 da kafuwa a jami'ar George Washington da ke birnin Washington, D.C.
A Senegal Ana sa ran kwararru 3000 ne zasu halarci taron kasashen Afirka akan cutar malaria domin tattaunawa akan yadda za a yaki cutar.
A Najeriya Iyayen daliban makarantar chibok da aka sace sun sake kira da a sako masu ‘ya’yansu a ranar da suka cika shekaru hudu da kungiyar boko haram ta sace su.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa Rasha ta kwan da shiri domin makamai masu linzami na nan zuwa Syria a wani matakin mayar da martani kan harin da ake na zargi amfani da makami mai guba.
Bayan da aka kwashe kwanaki ana mummunan tashin hankali tsakanin ‘yan tawaye da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin PK5, masu zanga-zanga sun jera gawarwaki a gaban ofishin Majalisar da ke Bangui.
Mazauna unguwar musulmi dake birinin bangui ta jamhuriyar afrika ta tsakiya na PK5 sun yi tattaki zuwa ofishin majalisar dinkin duniya dake jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
Domin Kari