‘Yan kasar Mali sun yi zaben fidda gwani jiya Lahadi yayinda aka tsaurara matakan tsaro don magance tashin hankali.
South Africa: Hamshakin dan kasuwa Alibaba wanda ya kirkiro kamfanin Jack Ma ya kaddamar da lambar yabo ta Netpreneur, wadda za a ba masu kananan sana’a’o’in da suka yi fice wajan kirkire kirkire
Chile: Jami’an ‘Yan Sandan kasar Chile na binciken sojoji malam addinin Krista da ake cewa Bishop masu gudanar da ayyukan ibada kan zargin lalata da kananan yara.
A Australia, mummunan fari da aka dade ba a gani ba, na barazana ga manoma a yankin New South Wales. Firai minista Malcolm Turnbull ya bada umurnin a ba manoma tallafin dala miliyan 140.
Wani shirin na samar da wutar lantarki, da gwamnatin Uganda da hadin guywar kasar China suka dauki nauyinsa, zai taimaka wajen rage matsanancin karancin wuta da ake samu a Uganda, zai kuma taimaka wajen habbaka tattalin arzikin kasar.
A Amurka wani dan bindiga ya budewa wasu ‘yan sanda guda biyu wuta a yayin da suke zaune cikin motocinsu.Sun tsira amma da raunuka kuma hukumomi sun ce dan sanda guda ya yi sa’ar mayar da wuta.
Zakaran wasan motsa jiki a shekarar 2015, Nicholas Bett ya rasa ransa a wani hadarin mota kusa da gidansa da ke yammacin Kenya.
A Najeriya mayakan Boko Haram suka kashe mutane 7 a cikin wani kauye dake arewa maso gabashin kasar, inda suka bude wuta da harsashen bindiga da gurnati akan motoci da babur.
A kasar Italiya jami'an gwmanati ke ci gaba da bincike akan wani mumunan hadarin mota da yayi sandiyar rasuwar mutane 14 da raunata wasu da dama a yammacin Italiya.
A Sudan ta Kudu inda shugaba Salva Kiir tare da shugaban yan tawaye Reik Machar suka sa hannu akan wata yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma raba madafun iko, da nufin kawo karshen yakin basasar shekaru biyar da suka gabata
A kasar Philippine shugaba Rodrigo Duterte ya bada sanarwar wata doka ta baiwa Musulmi yammancin yankin yancin walwala domin kawo karshen tashe tashen hankula da suke yi domin samun yancin kai
Zimbabwe: Jami’an tsaro na sintiri akan tituna suna korar ‘yan jarida wajan mayar da martani kan nasarar da shugaban kasa mai rikon gado Emmerson Mnangagwa yayi
Mali: Shugaban ‘yan adawa Soumaila Cisse yayi zargin an tafka magudi yayinda babu wanda ya sami kashi 50 na kuri’un da aka kada tsakanin sa da shugaba Ibrahim Boubakar Keita a zaben shugaban kasa. Za a sake gudanar da zaben a watan Agusta
Domin Kari