Palestine: An hallaka dan Isra’ila guda da kuma jikkata wasu biyu ta hanyar daba masu wuka da wani bafalasdine dake neman mafaka a Isra’ila yayi a yankin West Bank.
Nigeria: Kamfanin Google ya kaddamar da yanar gizo kyauta a wasu wurare daban daban da zummar samar damar amfani da yanar gizo a daukacin kasar wadda kusan kashi kashi 26 cikin dari na ‘yan kasar suka fara amfani da yanar gizo a shekarar 2016.
An soma wassanin kwallon hannu na VolleyBall ko tulla doke na kasa na maza da mata 'yan kasa da shekaru 17 na jahohin Nijar 8 da wadansu gundumomi da ke wakana a Birni N'Konni.
A Kasar China inda wani karamin bom ya tashi a bakin ofishin jakadacin kasar Amurka dake Beijin, ya jikkata maharin kadai.
'Yan gudun hijria fiye da dari 7 ne suka yi cincirindo kan shingen iyakokin Morocco da yankin arewacin Spain wato Ceuta da ya yi sanadiyar jikkata mutane fiya da dari
Hadakar Kungiyoyin Mata Musulmi Na Jamhuriyar Nijar, Da Ake Kira CONGAFEN Sun Yi Wani Taro Domin Neman Yadda Za a Magance Matsalar Shaye-shaye.
Canada: ‘Yan sanda a Toronto sun ce wani mutum dauke da bindiga ya harbi mutane 14, ranar lahadi, mutune biyu sun mutu, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar maharin.
Rwanda: shugaba Paul Kagame, ya marabci shugaban kasar China Xi Jimping, wanda ya isa Kigali domin ziyarar kwanaki biyu a cikin tafiye tafiyen sa Nahiyar Afirka da hadaddiyar daular larabawa.
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya gana da ministan tsaron kasar faransa Florence Parly, dake ziayarar aiki domin tattaunawa akan G-5 Sahel dake yankin.
A Switzerland kakakin Majalisar Dinkin Duniya yayi kiran gagawa ga dukkanin bangarorin kasar Syria dake rikici da juna su samawa ‘yan gudun hijira dubu 140 hanya.
Domin Kari