Dubban ‘yan kasar Habasha mabiya dadaddiyar akidar cocin kasar sun taru a Addis Ababa, babban birnin kasar, a karshen makon nan don bikin tunawa da baftismar Yesu Kristi.
Taskar VOA: Shugaba Muhammadu Buhari Na Jam’iyyar APC Da Alhaji Atiku Abubakar Na Jam’iyyar PDP Sun Yi Magana Akan Rikicin Makiyaya Da Manoma
Nijeriya: Wani shirin sauraren sautin cikin jiki da aka kirkiro a kasar Uganda ne ya lashe lambar yabo ta $ 25,000 a wata gasar da a turancin Ingilishi ake kira "TechCrunch Startup Battlefield Africa 2018" da aka gudanar a Lagos, Najeriya
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bada sanarwar shirya taron tattaunawa da shugabannin gwamnatin Amurka game da girka wani "yankin tsaro" a kan iyakokinta da Siriya bayan wasu hare-haren da aka kai kwanan nan a arewacin Syria.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce kokarin da Iran ta yi na harba tauraron dan Adam zuwa duniyar wata a jiya Talata, ya sabawa dokar MDD ta 2015.
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, ya cewa an shawo kan harin yan’taddan da ya hallaka mutane 14 a wani otel da ke birnin Nairobi.
Burkina Faso: Akalla mutane 50 aka kashe sannan wasu dubbai suka rasa muhallansu a wani rikicin kabilanci da ya faru a Burkina Faso.
Netherlands: A Netherlands, Wasu Alkalai a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, sun wanke tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo daga zargin aikata laifukan yaki, inda suka nemi da a sake shi ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya sa masu goyon bayansa suke ta murna a birnin Abidjan.
An rantsar da sabuwar majalisar dokoki a Amurka a makon da ya gabata, wata tsohuwar yar gudun hijira daga Kasar Somlaiya, Ilhan Omar ta hadu da Rashiba Tlaib, wata ba-amarkiyar ba-falasdiniya, sune suka zama mata musulmi na farko da suka shiga majalisar wakilan Amurka.
Masar: Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya hadu da takwaran aikinsa na Masar, Sameh Shoukry, inda ya jaddada cewa Amurka ta himmatu wajen ganin an yaki ayyukan ta'addanci a yankin.
A Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, dan takarar shugaban kasa a bangaren ‘yan adawa Martin Fayulu ya ce an tafka magudi a zaben da ya bai wa Felix Tshisekedi nasara, wanda shi ma daga bangaren ‘yan adawa ya fito.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa da Musulmi da Kirista sun san da cewar babu inda addinin Islama yace a kashe wani, kuma ayi kabbara. Ya kuma yi karin haske akan matakan da gwamnatinsa ke dauka na ganin an inganta tsaro a kasar.
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna gazarwar gwamnati mai ci kan matakan da take dauka wajen tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, musamman yadda satar jama'a don neman kudin fansa yayi yawa.
Yayin ziyarar da yake yi a kasar Jordan, Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya mayar da hankali kan tattauna batun Iran da kungiyar IS, a ci gaba da rangadin wasu kasashen Gabas ta Tsakiya da yake yi.
Hira ta mussaman da Aliyu Mustaphan Sokoto ya yi tare da manyan ‘yan takarar zaben shugaban kasa a Najeriya wato Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP sun yi magana akan wasu muhimman batutuwa.
Domin Kari