A Amurka wasu manyan motocin trela biyu tare da wasu safa-safa biyu sun yi taho-mu -gama a jihar Florida, lamarin da ya yi sanadiyar tashin wuta da ta halaka mutane bakwai a ranar Alhamis.
Kasar Somaliya wakilin kasar a majalisar dinkin duniya ya cewa majalisar da kada tsoma baki a harkokin kasar, kwamaki biyu bayan da kasar ta kori wani babban jami’in MDD a kasar.
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna gazarwar gwamnati mai ci kan matakan da take dauka wajen tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, da kuma yadda shi zai tunkari matsalar Boko Haram idan aka zabe shi.
A Burundi, inda Ginette Karirekinyana ta kirkero da mai na shafawa da wasu kayayyaki da ta yi ikirarin zasu taimaka wajen dakile cutar masassarar cizon sauro, saboda sinadiran dake cikinsu na korar sauro.
Kafafen yada labaran China sun sanar da cewa wani jirgin saman zuwa duniyar wata ya sauka lami lafiya karon farko a wani wuri nesa da wata.
Kungiyar Chelsea ta sayi dan wasan Amurka Christian Pulisic daga kungiyar Borussia Dortmund kan farashin Dala miliyan 73.2.
A kasar Sudan, a jiya talata jami’iyyun siyasa da wasu kungiyiyo 22 suka ce za su yi kira ga shugaba Omar Al-Bashir da ya yi marabus daga mukaminsa ya kuma mika iko ga wata “majalisa mai cin gashin kanta” da gwamnatin wucin gadi da za su shirya zabe karkashin turbar Dimokradiyya.
A jihar Plato dake Najeriya. Wasu matasa biyu sun bude wani ofishi a cikin birnin Jos inda suke taimakawa matasa da shawarwari dabam dabam, musamman masu mu’amulla da miyagun kwayoyi
Daga karshe sai kasar Peru, inda mutane a kalla 8 su ka mutu baya ga 20 da su ka ji raunuka bayan da motar bus din da su ke ciki ta abka cikin wani kwari daura da birnin Huancayo.
Bayan da aka ayyana Andry Rajoelina a matsayin wanda ya ci zagaye na biyu na zaben Shugaban kasar Madagasca, mai karawa da shi Marc Ravalomanana ya yi kiran da a soke zaben a wata karar da ya kai babbar kotun kundin tsarin mulkin kasar
Bukin Kirsimeti a Birnin N'Konni da irin rawar da hukumomi suka taka, na baza jami'an tsaro domin kariyar lafiya jama'a da majami'u, haka al'ummah Musulmai sun yi ma Kiristoci barka da shagulgula.
A kasar Sudan ‘yan sanda suka harba borkonon tsofuwa akan masu zanga zanga da ke shirin yin tattaki zuwa fadar shugaban kasar, domin neman shugaba Omar Al-Bashir ya yi marabus.
A kasar Indonesia masu ayyuka ceto na amfani da jirage marasa matuka da karnuka wajen ci gaba da neman mutane fiye da 100 da suka bata, bayan bala’in tsunami da ya abkawa gabar tekun Java da kudancin Sumatra, lamarin da ya kashe mutane 429.
Domin Kari