Amurka: Shugabn Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabin sa na biyu, kan halin da kasa ke ciki, a gaban majaliisar dokokin kasar, dake zaman a farko da zummar raba kan ‘yan jam’iyyar Democrats masu rinjaye
Thailand: Hukumomi suna amfani da jirage masu sarrafa kansu don magance abinda hukumar sa ido akan yanayi a kasar Thailand ta kira “mummunan gurbatar yanayi a Bangkok.”
A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya: yau Alhamis ne wa’adin Takunkumin makaman da MDD ta sanya akan dakarun jamhuriyar Africa ta tsakiya zai kare, kwanaki 3 bayan da wani gangami da Firayim Ministan kasar ya jagoranta ya bukaci a dage takunkumin da aka sanya tun shekarar 2013.
Dazu da maraice shugaban Najeriya ya kammala ziyarar yakin neman zabe a Kano, sai dai shugaban bai yi wani sabon alkawari ba musamman ta fuskar lamuran da suka shafi farfado da masana'antun Kano da harkokin kasuwanci.
Masu tattaunawa daga kasar China da Amurka sun gana a yau Laraba don tattaunawar a karo na biyu da nufin daidaita matsalar cinikayya tsakanin kasashen biyu.
Yau Laraba Jami’an tsaro suka rike ‘yar shugaban ‘yan adawan Sudan Sadiq al-Mahdi na wani ‘dan lokaci, duk kuwa da zanga-zangar nuna rashin amincewa da gwamnati da kasar ke fama da ita.
Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya kawo ziyara nan Amurka kuma Aliyu Mustapha ya sake ganawa da shi anan sashen Hausa akan wasu batutuwa.
A Amurka, an kama tsohon mai bai wa shugaba donald Trump shawara akan harkokin yakin neman zabe a yau juma'a, saboda zarge-zargen aikata manyan laifuka da dama a bincike na musamman da ake yi game da katsalanan din Rasha a zaben Amurka na 2016.
shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa da firaministan kasar India Marendra Modi sun kulla yarjejeniyar huldar kasuwanci ta tsawon shekaru uku a birnin New Delhi
Venezuela: Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace jami’an diflomasiyyan Amurka bazasu bar kasar Venezuela ba bisa dokar da shugaban kasar Nicolas Maduro ya bada a ranar laraba da ta basu awowi 72 na su bar kasar.
Najeriya: Babbar 'yar takarar shugaban kasa mace ta Najeriya Oby Ezekwesili ta janye daga takarar zaben shugabancin kasar don taimakawa wajen hada hancin sauran jam’iyyun siyasa don yin adawa da manyan jam'iyyu na kasar.
Qatar: Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yana ziyarar a kasar Qatar don neman goyon baya, yayin da ake cikin zanga-zangar adawa da mulkinsa da ya kwashe shekaru 29 yana yi.
Turkiyya: Magoya bayan jam'iyyar HDP sun taru a kofar wani kurkuku yayin da shugaban jam’iyyar ke jiran karar da aka shigar da shi kan ta’addanci da ake ganin na da nasaba da farfaganda.
Domin Kari