Biritaniya: Firayim Minista Boris Johnson ya ce muhimmin abinda gwamnatinsa ta sa gaba shi ne "ficewar Birtaniya daga Turai," yana mai alkawarin barin Tarayyar Turai a ranar 31 ga Oktoba "ko ta wata hanya," a ranar karshe na taron jam’iyya masu ra’ayin rikau.
Mali: An kashe Sojin Mali 25 kuma guda 60 sun bace bayan wani harin da ake zaton masu jihadi ne suka kai kan sansanonin sojoji biyu a tsakiyar Mali a ranar Litinin. Adadin wadanda suka mutu na daga cikin babban harin da sojojin suka fuskanta a bana.
Mayakan kungiyar Al-Shabab a Somaliya sun dauki alhakin kai wasu hare-hare biyu kan sansanin sojin Amurka dake Baledogle da kuma wani jerin gwanon motocin ‘yan Italiya a kusa da Mogadishu.
Shugaban Ukrain, Volodymr Zelenskiy ya ce ba lalle bane ya saki bayannan hirar waya ta ranar 25 ga watan Yuli tsakanin sa da Shugaban Amurka Donald Trump yayin da ake yunkurin tsige trump.
Rundunar Soji Ta Kori Jami'anta Su Uku, Wandanda Ake Zargin Cewa 'Yan Kungiyar Asiriri Ne A Maiduguri
Muryar Amurka ta zanta da sabon jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya kuma shugaban majalisar zartarwa na zama na 74, farfesa Tijjani Muhammad Bande
Amurka: Shugaba Donald Trump ya mayar da martani ga wakiliyyar ‘yan democrats, Nancy Pelosi game da binciken tsigewan shugaba a hukumance, abin da ya kira " cigaban bita da kulin siyasa" bayan da aka yi zarge-zargen cewa ya nemi taimakon kasashen waje, wajen sake zabensa na 2020.
Aljeriya: Bouteflika, dan uwan tsohon shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika, yace an yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a kurkuku tare da wasu masu kare shi su uku, bayan da suka hada baki da nufin sauya mulki, a cewar wata kotun sojan Algeria.
Tun shekara ta 2000 rayuwar mutane masu fama da matsanancin talauci a duniya ta inganta amma har yanzu ana fama da rashin daidaito a fannoni da dama. Wannan, shine bayyanan da rahoton gidauniyar Bill da Melinda Gates ya kunsa da ya shafi shirin raya kasashe na majalisar dinkin duniya.
Kamfanin tafiye-tafiye ta Thomas Cook ta ba da sanarwar fatarar kudi bayan ta kasa cimma yarjejeniyar ceto, lamarin da ke haifar da koma baya ga Birtaniyya tun bayan Yaƙin Duniya na II don dawo da dubun matafiya.
A kalla yara 7 sun rasa rayyukan su, bayan da wani gini ya ruguzo musu a wata makaranta a Nairobi babban birnin kasar Kenya
Kasar Saudiyya ta shiga rundunar hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta don tabbatar da kare hanyoyin ruwan ‘kasa da kasa biyo bayan barazanar Iran, bayan harin da take kaiwa kamfanonin Mai.
Masanan kimiyya a Burkina Faso sun dauki wani sabon matakin da za a iya yaki da zazzabin cizon sauro, tare da sakin dubban wasu sauro da ake ikirarin basa dauke da kwayoyin cututtuka da ke cutar da bil adama, wanda ya haifar da muhawara mai zafi dangane da abinda ya shafi halittu.
Sabon Ministan Tsaron Najeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi ya kai ziyara Maiduguri. Yankin da ya dade yana fama da matsalar ‘yan Boko Haram.
Za a yi zaben shugaban kasa a Tunisia jibi Lahadi. ‘Yan takarar shugaban kasa sun yi wata muhawara a karon farko a farkon watan nan, inda suka tattauna batutuwa ciki har da tattalin arziki da tsattsauran ra’ayin addinin Islama.
Domin Kari