Adadin mutanen da su kamu da Coronavirus ya karu zuwa sama da mutum 6,100 a fadin duniya yayin da China ke da adadin mutum 132 da suka mutu. Adadin mutun 6,060 da suka kamu a Chinar, ya haura jama’a da suka kamu da cutar SARS a lokacin annobar na 2002 zuwa 2003, wacce ta kama mutum 5,327