A Birtaniya Yerima Harry da uwargidansa Meghan Markle, sun ba da sanarwar janyewa daga jagorancin ayyukan masarautar kasar, domin tafiya neman na kansu, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umar kasar.
A kasar Libya kuma, ministocin harkokin wajen kasar Faransa, Masar, Girka da kuma Cyprus sun nuna adawarsu da matakin da Turkiyya ta dauka na tura dakarunta zuwa Libya.
A Iran, akalla mutum 40 suka rasa rayukansu kana wasu 200 suka jikkata, bayan wata turereniya da ta auku a lokacin jana’izar Qassem Soleimani, a cewar kafar talbijin din kasar.
A Najeriya, akalla mutum 30 suka mutu bayan da wani bam ya tashi a wata gada a garin Gamboru da ke jihar Borno.
Shugaban addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya jagoranci addu’o’in da aka gudanar yau litinin don Qassem Soleimani yayinda dubban jama’a suka taru a Tehran don alhinin mutuwar babban Janar din na Iran.
A Kenya, An kashe Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka guda 3 yayin da kungiyar ‘yan ta’addan al-Shabab dake Somaliya ta mamaye wani muhimmin sansanin soja da dakarun Amurka dake yaki da yan ta’adda ke amfani da shi a Lamu, kafin wayewar garin jiya Lahadi.
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi tattaki har zuwa kasar Niger domin jajantawa gwamnatin bisa rashin sojojinta 71, kana ya karrama wadannab maza da suka kwanta dama.
Akasar Indiya ‘yan sanda su ka tsare masu zanga-zanga fiye da dari a yau alhamis bayan da suka keta wata doka wacce hukumomi suka sa ran zata magance zanga-zangar kin jinin wata sabuwar dokar da ke da nasaba da takardar zama ‘yan kasar.
A karshe kuma, shugaban Rasha Vladimir putin ya bayyana cewa yana son ya ga an kawo karshen rikicin da ake fama da shi a Libya.
A Pakinstan, inda wata kotu ta musamman ta yanke wa tsohon shugaban kasar Pervez Musharaf hukumcin kisa bayan da aka same shi da laifin cin ammanar kasa.
A Gambiya, dubun dubatun jama'a su ka yi tattaki a Banjul babban birin kasar, inda su ke kiran Shugaba Adama Barrow da ya yi murabus daga mukaminsa.
A Nijar, shugabanin kashen yankin G5 Sahel sun yi kira da a hada kai sosai a kuma bayar da goyon baya a matakin kasa da kasa a yakin da ake yi da masu tsattsauran ra’ayin addini, a wani babban taronsu a Yamai.
A Kasar Spain, an kammala taron Majalisar Dinkin Duniya na mafi tsawon lokaci kan matsalar dumamar yanayi da kasashen da su ka yi alkawarin kara rage yawan sinadarin carbon da su ke amfani da shi badi.
Anan Amurka, ‘yar Majalisar wakilan Amurka daga Florida Federicka Wilson ta shirye wani taro don jan hankalin gwamnatocin kasashen duniya, da su tuna da ragowar ‘yan matan Chibok da har yanzu ba a kubutar ba. Ga rahoton da abokiyar aikinmu Grace Oyenubi ta hada mana.
A Birtaniya masu zabe zasu kada kuri’a a yau wanda ke da nasaba da ficewar birtaniya daga tarayyar turai, wanda aka jima ana ta sa in sa a kansa.
A jamhuriyar Nijar, Bayan da mayaka suka kashe sojoji 71 a wani kazamin hari da suka kai a wani sansanin sojin kasar da ke kusa da iyakarta da Mali, wani mai Magana da yawun rundunar y ace wannan shi ne hari mafi muni da aka taba kaiwa kan rundunar sojin ta Nijar.
BIDIYO: Ra'ayoyin Jama'a Kan Mumunan Harin Da 'Yan Ta'adda Suka Kai Inates Wanda Ya Yi Sanadin Mutuwar Sojoji Akalla 70
A Afghanistan, wani bam ya ruguza wani ginin asibiti da ba a kammala ba da ke kusa da sansanin sojojin saman Amurka da ke Bagram, arewacin Kabul babban birnin kasar. A kalla ‘yan kasar shida ne suka raunata.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ce al’amarin canjin yanayi shi ne asalin dukkannin tashe-tashen hankula a yankunan Afurka, ya yi kuma kira na musamman kan yaki da cin hanci da rasahawa a lokacin da ya halarci babban taron Aswan da aka yi a kasar Masar.
Domin Kari