A Turkiya, wani jirgin sama na soja wanda ke dauke da kayayyakin agaji na jinya, da na kariyar lafiya ya tashi daga Ankara zuwa Amurka, wacce take kawar Turkiyar, a kungiyar NATO.
A Najeriya Shugaba Buhari ya ce za a fara sassauta dokar hana zirga-zirga ta coronavirus a manyan biranen kasar, Legas da Abuja daga ranar 4 ga watan Mayu.
Sai Birtaniya, A karon farko Firaiministan Boris Johnson ya yiwa kasar jawabi a wajen Downing Street tun bayan da aka kwantar da shi a asibiti saboda Covid-19.
A Afirka ta Kudu, akalla likitocin Cuba dari biyu suka isa kasar ranar Litinin domin taimakawa a yaki da Covid-19.
A Amurka, kamfanin Lysol ya gargadi mutane da su guji shan sinadarin tsaftace muhalli bayan shugaba Donald Trump ya nuna cewa idan aka sha zai taimaka wajen warkar da wanda ya kamu da coronavirus.
Hukumomin kasashen Afirka ta yamma sun amince da Umar Sissoco Embalo a matsayin shugaban kasar Guinea-Bisau, bayan wattanni 4 ana takaddama a game da zaben kasar.
A Vietnam kuwa: Al'amurra sun fara komawa dai-dai, bayan kulle na tsawon makonni ukku, a yunkunrin dakile yaduwar COVID-19. Kasar ba ta samu wani sabon wanda ya kamu da cutar ba cikin mako guda.
A Madagaska Dalibai sun koma makaranta, bayan hutun wata daya, tare da basu kyautar magungunan gargajiya domin samun kariya, a cewar shugaban kasar Andry Rajoelina.
A wani Jawabin kasa na musamman, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril RAmaphosa ya sanar da shirin yaye na dala biliyan 26 da zummar tallafawa tattalin arzikin kasar da kuma mutane masu rauni a yayin da ake fama da coronavirus.
A Amurka, ana sa ran shugaba Donald Trump, zai rattaba hannu a wata dokar wucin gadi da za ta dakatar da shigar baki kasar a ranar Laraba.
A Jamhuriyar Demokradiyya Congo akalla mutane 25 ne suka mutu sannan kusan gidaje 3,500 suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa a gabashin kasar.
Lucy Jones, hafafiyar Wales ce da ta kafa kamfanin dinka sittirun kawa na musamman a birnin New York – ta mayar da hankali ne akan dinka sitturu don nakassasu.
Mutane da suka rasa matsugunansu a arewa maso gabashin Najeriya sun yi cincirindo yayin da ake raba abinci da kudi a wani sansani. Aƙalla mutane biyar sun mutu a turmutsitsi.
A kasar Denmark Ofishin Hukumar lafiya ta duniya da ke Turai ya ce "duk da alamun nasara" a kasashen da annobar COVID-19 ta yi kamari, ana kara samun yaduwar ta, inda yanzu haka a nahiyar kawai ake da kusan mutum miliyan daya.
A Najeriya inda yunwa da bacin rai ke karuwa a Lagos da ma wasu manyan birane a Afrika da basu da matakan ragewa jama’a radadin matsalolin da COVID-19 ta janyo.
Shugaban Guinea Alpha Conde ya ce dole ne mutane su rika amfani da takunkumin kariya na fuska a kasar a kokarin dakile yaduwar coronavirus.
shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya zargi WHO da yin sanadin ninninka yaduwar cutar COVID-19 a fadin duniya, ya dakatar da baiwa Kungiyar ta Lafiya ta Duniya agajin kudi.
Domin Kari