A Najeriya Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita dokar hana fita a Abuja, Legas da Ogun na tsawon makwanni biyu, a kokarin shawo kan yaduwar cutar coronavirus.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za a tsawaita dokar hana zirga-zirga a kasar zuwa 11 ga watan Mayu, don rage yaduwa Coronavirus, amma ya ce za a iya fara sassauta matakan, daga wannan lokacin, idan abubuwa suka fara yin kyau.
Ma’aikatar harkokin wajen China ta ce an dauki wasu sabbin matakai domin inganta yadda ake kula da 'yan Afirka a garin Guangzhou da ke kudancin kasar sakamakon zargin nuna musu wariya dangane da annobar coronavirus.
Fafaroma Francis ya yi addu’a ranar Litinin a bikin Ista ga masana kimiyya da ‘yan siyasa ta yadda za su kawo ƙarshen coronavirus don ya zama alheri ga mutane ”.
Duk da gargadin da ake yi, wadansu mutane a Afrika suna ta rububin sayen maganin kulorokwin da ake amfani da shi wajen maganin zazzabin cizon sauro, da ya sa aka shiga karancinshi a kantunan sayar da magunguna
Jihohi da dama a najeriya suna ci gaba da daukan matakai na yaki da cutar coronavirus. A jihar kano, duk da cewa gwamnati ba ta hana mutane walwala ba, akwai dokar hana mutane shiga jihar daga wata, sannan ana gudanar da feshi na kashe cutar ta coronavirus.
An dauke Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson daga dakin ‘yan-gobe-da-nisa bayan da ya dan murmure daga alamomin cutar Coronavirus da yake fama da su.
A Amurka cutar coronavirus na ci gaba da kisan Amurkawa 'yan asalin Afirka fiye da 'yan Amurka, a cewar alkaluman farko da jami'ai suka ce sun nuna banbance-bambancen matakin lafiya da samun ayukan kiwon lafiya.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bukaci assusun ba da tallafi na Duniya IMF da ya amince da bukatarsu na bashin gaggawa na dalar Amurka Biliyan 5 domin yaki da cutar coronavirus. Ana sa ran kasar Amurka tayi kokarin hanawa.
A nan Amurka wasu 'yan siyasa da likitoci, suna tayar da jijiyar wuya, a game da ko za a yi amfani da chloroquine, wajen warkar da cutar Coronavirus, inda akasarin masana kimiyya suka ce ba bu kwakkwarar hujja ta yin hakan.
A kasar Kamaru Jami'an birnin a Douala, suna ba da takunkumin rufe baki da hanci, da share hanyoyi don hana yaduwar COVID-19.
Biritaniya: Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson, wanda ya kamu da cutar coronavirus a makon da ya gabata, ya na ci gaba da zama a asibiti a Litinin din nan, bayan ya ci gaba da fama da zazzabi mai zafi.
Libya: Mahmud Jibril, tsohon shugaban 'yan tawayen da suka hambarar da shugaban Libiya Moammar Ghadhafi, a 2011, ya mutu ranar Lahadi sakamakon coronavirus.
A Najeriya kuma, da alamu hukumomi sun fara shawo kan matsalar rashin aiki da dokar zama a gida da wasu a wasu wurare don yaki da cutar Coronavirus. Da farko dai wasu malaman addinai sun nuna basu yarda akwai cutar ba, abin da ya sa suka ki mutunta dokar zama a gida da aka sa.
Domin Kari