Duk da cewa mutanen da suka kamu da cutar a nahiyar Afirka basu kai yawan na sauran nahiyoyi ba, cutar tana babbar barazana a wasu manyan kasashen Afirkan, yayin da take ci gaba da yaduwa. A yau mun gayyato kwarru daga wasu kasashen Afirka da nan Amurka da za su amsa wasu daga cikin tambayoyinku.
A kasar Kenya, daruruwan masu zanga zanga ne suka mamaye titunan da ke wajen babban birnin kasar Nairobi yau juma’a don nuna bacin ran su bayan da jami’ai suka rusa musu gidaje da kantuna da ake zargin akan filin gwamnati aka gina.
Yayin da azumin watan Ramadana ya kankama a duk fadin duniya, mallamai na ci gaba da tunatar da al’ummar Musulmi game da abubuwan da ake bukatar daga wurinsu. Ga Sheikh Jabir Sani Mai-hula Sokoto.
A kasar Iran, shugaba Hassan Rouhani yayi kashedi ga mummunar sakamako idan aka cigaba da dora haramcin makamai a kan Tehran, bayan shugaba Trump yayi watsi da yarjejejniyar nukiliya.
A Morocco kuma, kasar ta kara yawan jiragenta mara matuka a yaki da take yi da annobar coronavirus, wanda zasu rika sa ido a unguwanni, da ayyukan sanar da jama’a da kuma tsafatace muhalli
A Najeriya ‘yan sanda a Legas sun kama mutane da ake zargi, da karya dokar hana fita da gwamnati ta kafa a daren Litinin. An bude wasu sana’o’i yayin da aka sauƙaƙa dokar hana fita ta COVID-19 a wasu biranen.
A Indiya,hukumomi suka fara sassauta dokokin hana zirga zirga na Korona Biros duk da wadanda suke kamuwa yana karuwa. Wasu dokokin za su c igaba har zuwa 18 ga watan Mayu.
A Najeriya, inda aka fara sassauta dokar hana zirga-zirga a babban birnin kasar Abuja da kuma jihar Legas, abin da ke alamta sake bude tattalin arzikin kasar wanda shi ne mafi girma a Afirka bayan sama da makonnin hudu.
A yau Juma’a a birnin Beijing,an bubbude wuraren shakatawa, gidajen kayan tarihi da ya hada da tsohon haramtaccen birni bayan da suka kasance a rufe na watanni saboda annobar coronavirus
A Faransa shahararren makadi ‘dan Najeriya Tony Allen, wanda sukayi tashe da shahararren mawaki Fela Kuti yamutu jiya alhamis a Paris yana da shekaru 79.
A kasar Guinea kuwa: An dauki shatar wani jirgin sama don ya dauko magungunan gargajiya 11,500 na cutar coronavirus da kasar Madagasaka ta ce ta samar.
sojan sama da sojan ruwan Amurka suka yi shawagi a sararin samaniyar birnin New York da New Jersey da kuma Philadelphia domin jinjinawa ma’aikatan lafiya da masu bada muhimman ayyuka dake sahun gaba a yaki da coronavirus.
Kasar Senegal ta fara rabon kayan abinci domin taimakawa miliyoyin mutane dag alibi masu karafin karfi ne da coronavirus ta addabesu.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, akwai sama da ‘yan gudun hijira miliyan 30 a kasashen duniya, galibi suna zama a yanayin da cutar coronavirus zata iya yaduwa cikin sauki.
Domin Kari